1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RONALD REAGAN TSOHON SHUGABAN AMURKA YA RASU YANA DA SHEKARU 93.

HOTON MARIGAYI REAGAN KE NAN DAYA JAGORANCI MULKIN AMURKA NA TSAWON SHEKARU TAKWAS.

default

A ranar asabar din data gabata ne dai tsohon shugaban kasar ta Amurka na 40,wato Ronald Reagan ya rugamu gidan gaskiya bayan yasha fama da matsananciyar cutar sanyi da kuma wasu kana nan cututtuka yana da shekaru 93 a duniya.

Ronald Regan wanda akafi sani da kaboy ya taba zama gwamnan jihar Califonia daga shekara ta 1967 izuwa shekara ta 1975.

A cikin rayuwar sa Reagan ya kasance fitaccen dan siyasa kuma mai iya magana cikin hikima wanda hakan nema yasa Amurkawa sujka zabe shi a matsayin shugaban kasar ta Amurka a shekara ta 1980 a karkashin tutar jamiyyar Republican Bayan ya kayar da shugaba maici a wancan lokaci wato Jimmy Cater.

Bisa irin taka rawar da Reagan yayi wajen warware rikice rikice daci gaban al,ummar duniya musanmamma Amurka shugaba Bush na Amurka ya bayar da sanarwar kebe ranar juma,a mai zuwa a matsayin ranarhutu da girmamawa ga tsohon shugaban na aMurka.

Yayin da yake jawabi a bikin nuna alhini na zagayowar ranar da dakarun kawance suka afkawa dakarun sojin Haetler a tsibirin Nomandi,Shugaba Bush na Amurka ya bayyana Ronald Reagan a matsayin shugaba mai dattako da kwazo wajen iya aiki da kuma rashin nuna kasala wajen daukar matakan samar da yancin fadar albarkacin baki.

Haka shima tsohon shugaban kasar Amurka da Ronald Reagam ya karbi ragamar mulki a hannun sa,wato Jimmy Cater ya tabbbatar da cewa mutuwar Jarimi Ronald Regan ba karamar asara bace ga Amurka da kuma ma duniya baki daya,bisa namijin kokarin daya nuna wajen dinke barakar dake akwai lokacin yana mulki.

Bugu da kari sauran shugabannin duniya masu fada aji irin su Shugaba Schroder na Jamus da Jack Chirac na Faransa da kuma Vladimir Putin na Rasha da Tony Blair na biritaniya , dukkannin su sun nuna alhini na rashin shugaba gogan gayya kuma jarimi a wajen aiwatar da matan kawo sulhu a duniya.

Har ila yau a waje daya tsohon shugaban gwamnatin Jamus Helmut Kohl da tsohon shugaban kasar tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev sun koka dangane da rashin Ronald Reagan bisa mihimmiyar rawa daya taka na kawo karshen yakin cacar baka a duniya a hannun daya kuma da taimakawa wajen ganin nahiyar turai ta zama uwa daya uba daya.

Shima shjugasban darikar Katolika na duniya Pope John Paul na 2 yace babu shakka anyi rashin mutum mai iya magana daya taimaka wajen canja rayuwar miliyoyin mutane a nahiyar turai.

Shi kuwa dan takarar neman shugaban Amurka a karkashin tutar jamiyyar Demokrat John Kerry cewa yayi ya dakatar da kamfe din sa a wan nan makon kwata kwata don nuna alhini da mutuwar tsohon shugaban bisa gagarumar gudun mawear daya bayar a lokacin yana mulkin kasar ta Amurka ta fannoni daban daban na rayuwa.

A daya barin kuwa Shugaba Mohd Ghaddafi na Libya cewa yayi kamata yayi ace an gurfanar da marigayi Regan a gaban kotu a tun yana da rai bisa ruwan bama bamai da yaya bayar da umarni ayi a kasar libya a shekara ta 1986.

Shugaba Ghaddafi ya kuma ta,allaka rikice rikicen dake ci gaba da faruwa a yankin gaba ta tsakiya da cewa marigayi Ronal Regan ne ya haifar dasu a tun lokacin yana gadon mulkin shugabancin Amurka.

Haka shima tsohon wakilin kasar Syria a mdd Haitham Al Kilani raaayin sa ya bayyana da cewa matakan gwamnatin marigayi Ronald Regan matakaine da suka kai yankin gabas ta tsakiya suka baro,wanda hakan a yanzu ya haifar da rasa gano bakin zaren.

Mai dakin marigayi Reagan wato Nancy Reagan ta hannun kakakin iyalan nasa godewa dubbannin Amurkawa dake jerin gwano wajen mika taaziyyar su ga tsohon shugaban na Amurka ta hanyar ajiye fulawowi da ire iren makaman tansu

A ranar juma,a mai zuwa ne dai ake sa ran kawo gawar Ronald Reagan izuwa fadar White house don karbar girmamawa ta karshe kafin a binne shi a dakin karatun sa dake gidan sa a jihar Califonia.