ROMANO PRODI YA KAWO ZIYARA A BERLIN | Siyasa | DW | 04.03.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

ROMANO PRODI YA KAWO ZIYARA A BERLIN

Shugaban Hukumar Kungiyar Hadin Kan Turai, Romano Prodi, ya nuna amincewarsa da shawarar da Jamus da Fansa da Birtaniya suka bayar, ta kafa wani reshe karkashin ofishin mataimakin shugaban Hukumar, wanda zai dinga kula da harkokin yi wa kafofin tattalin arzikin kasashen kungiyar garambawul. Prodi ya bayyana hakan ne, bayan wata ganawar da ya yi da shugaban gwamnatin tarayyar Jamus, Gerhard Schröder a birnin Berlin.

Romano Prodi, tare da shugaba Schröder a Berlin.

Romano Prodi, tare da shugaba Schröder a Berlin.

Romano Prodi, shugaban Hukumar kungiyar Hadin Kan Turai, ya kawo ziyara a nan Jamus ne don tattauna batun shawarar nan da shugabannin gwamnatocin muhimman kasashen kungiyar, wato Jamus da Faransa da Birtaniya, suka bayar game da kirkiro wani reshe karkashin ofishin mataimakin shugaban Hukmar, wanda zai dinga kula da batutuwan da suka shafi yi wa kafofin tattalin arzikin kasashen kungiyar Hadin Kan Turan garambawul. Bayan ganawarsa da shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder yau a birnin Berlin ne, Romano Prodi ya bayyana goyon bayansa ga shawarar kafa wannan reshen. Amma batun tsai da dan takarar da zai gaji shugaban kasa Johannes Rau ne, ya fi damun maneman labaran da suka halarci taron da Prodin ya yi wa jawabi bayan ganawarsa da Schröder.

Duk da hakan dai, shugaban Hukumar kungiyar Hadin Kan Turan, ya sami damar bayyana matsayinsa game da abin da ya kawo shi ziyara a birnin Berlin, wato na daidaita siyasar harkokin tattalin arzikin kasashen kungiyar. Shawarar dai aba ce mai kyau, inji Prodi. Amma Hukumar da yake yi wa jagoranci ba za ta iya aiwatad da kome ba a halin yanzu, sai bayan an zabi wanda zai gaje shi a cikin watan Nuwamba ne za a tattauna batun tsara shirin aiwatad da shawarar da kasashen jamus, da Faransa da Birtaniya suka bayar. Ya kara da cewa, a taron kolin da shugabannin kasashen kungiyar Hadin Kan Turan za su yi a karshen wannan watan ne, za a zayyana shirye-shiryen yi wa tattalin arzikin kungiyar garambawul, don farfado da shi. Game da kundin tsarin mulkin kungiyar da aka gabatar kuwa, shugaba Schröder ya bayyana cewa, kamata ya yi a tabbatad da shi karkashin ragamar jagorancin kungiyar da kasar Ireland ke ja a halin yanzu:-

"Da alamun za a iya yin hakan. Amma akwai kuma masu daddage wa shirin. Sabili da haka ne ba za mu iya yin hasashe kan nasarar samun karbuwarsa ba."

Shugaba Schröder dai ya yabi rawar da kasar Ireland ke takawa, wajen jagorancin kungiyar ta Hadin Kan Turai a halin yanzu. Game da shirin fadada kungiyar Hadin Kan Turan kuma, ya bayyana cewa:-

"Shugaban Hukumar kungiyar, ya fadakad da kansa game da tattaunawar da ake yi da kasashen Romaniya da Bulgeriya, ta neman shigowarsu cikin kungiyar, ya kuma nuna alfaharinsa da ci gaban da aka samu."

 • Kwanan wata 04.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlV
 • Kwanan wata 04.03.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvlV