Rokokin Hezbollah sun kashe yahudawa 8 | Labarai | DW | 16.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rokokin Hezbollah sun kashe yahudawa 8

Rokokin Hezbollah sun kashe yahudawa 8 a birnin Haifa yayinda bama bamai suke ci gaba da girgiza birnin Beirut kwana na 5 na hare hare da Israila ta kaddamar akan Lebanon.

Wannan dai shine hari mafi muni da Hezbollah ta kai Israila cikin shekaru 10 da suka shige.

Firaministan Israila Ehud Olmert yace abinda zai biyo baya ba zai yiwa Lebanon dadi ba.

Rokoki kusan 20 yan kungiyar ta Hezbollah suka harba a Haifa birni na 3 mafi girma a Israila,a matsayin martani dangane da kashe farar hula da Israilan take ci gaba dayi a Lebanon.

Saoi kadan bayan harin jiniyoyi sun tashi a birnin Haifa,domin fargar da mutane su nemi wuraren buya,saboda yiwuwar wasu hare haren kuma.