Rohingyas: Buwaya a damuna
Fiye da 'yan Rohingyas 400.000 sun gudu zuwa Bangaladash a karshen Agusta tun kafin sojojin Myanmar su far musu. Yanzu haka ruwan sama mai yawa a kan iyakokin kasashen biyu na jefa 'yan gudun hijira cikin mummunan hali.
Yanayi mai muni a sansanin 'yan gudun hijira
Karancin abinci, karancin tantuna - da yawan ruwan sama. Daruruwan 'yan Rohingyas na zaune a mummunan muhalli a Bangaladash. Sun yi gudun hijira ne daga makwabciyar kasar Myanmar, inda sojoji ke barazana ga rayukansu.
Ruwan sama na tsananta halin rayuwa
Tun ranar Lahadi, yanayi ya sa halin rayuwar 'yan Rohingyas ya dada tabarbare. A garin Cox Bazar kawai, a kan iyakar Myanmar da Bangaladash, an yi ruwa mai karfin gaske a cikin sa'o'i 24 na baya-bayanan. Ko kafinnan akwai karancin tantuna, yanzu mutane da yawa na rayuwa cikin ruwa. Ruwan sama ya haddasa ambaliya a sansanin tare haifar da laka.
Cibiyoyin agajin gaggawa sun cika makil
Mutanen da suka tsere wa rikici ba su da wurin da za su fake wa ruwan sama. Suna barci ne a sansanonin jeka na yi ka a kan hanyar Myanmar zuwa kasar Bangaladash. Ga shi kuwa ana sa ran cewar ruwan sama zai tsananta.
Karancin kayan agaji, musamman abinci
A kan hanya mafi girma ake samun kungiyoyin agaji da ke rarraba abinci da sauran kayayyakin agaji da ake bukata. Taimakon agaji na da muhimman saboda yankin "ba ya iya magance kalubalen kwararar 'yan gudun hijira," a cewar mai magana da yawun hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR.
Aikin tsugunar da 'yan Rohingya
Gwamnatin Bangaladash na shirin tsugunar da 'yan Rohingyas a wani sansani don samun saukin rarraba kayan agaji. Masu sukar gwamnati suka ce ya kamata a hana 'yan gudun hijira yaduwa a cikin kasar. A ranar Asabar, 'yan sanda sun haramta wa 'yan hijira fita daga yankunansu lamarin da ya sa wasu kasa zuwa wurin iyalansu, ko abokansu.
'Yan gudun hijira 410.000 a makonni hudu
Tun karshen watan Agusta, kimanin mutane 410,000 suka yi hijira daga Myanmar zuwa Bangaladash. A rikice-rikicen baya-baya dai 'yan Rahingyas 300,000 ne suka shiga cikin kasar. Sai dai mummunan yanayi, ya sa adadin da ke kwarara kasar ya ja baya, a cewar jami'an shige da fice na Bangaladash.
Rohingya sun zama baki a kasarsu
Rohingyas Musulmi ne marasa rinjaye a Myanmar, kasar da mabiya Buddha suka mamaye. Ba a daukansu a matsayin 'yan kasa, saboda haka ne ake nuna musu bambanci. Gwamnatin ta zargesu da shiga kasar daga Bangaladash, ko da shi ke suna rayuwa a Myanmar tun shekaru aru-aru. Majalisar Dinkin Duniya ta daukin rikicin Myanmar a matsayin yunkurin neman yi wa Rohingyas kisan kare dangi.
Rikicin ya fara ne a karshen Agusta
An samu sabon rukunin 'yan gudun hijira na Rohingyas bayan rikici da aka fuskanta tsakanin' yan bindiga da kuma soja. A 25 ga Agusta, 'yan tawayen Rohingyas suka hallaka sojojin gwamnati fiye da 12. Sai dai sojoji sun mayar da mummunan martani. Daruruwan mutane ne aka kashe, yayin da aka kona gidajensu. Ba a san lokacin da za a kawo karshen tashin hankali ba.
Akasarin 'yan gudun hijira yara ne
A cewar Asusun Tallafa wa Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, shida daga cikin 'yan gudun hijira goma yara ne, da yawa daga cikinsu na fama da tamowa. Sakamakon ruwan sama, da yawa daga cikinsu na fama da mura da tsanani cututtuka. Bangaladash na shirin yi wa yara 150,000 rigakafin cutar kyanda, da Polio a cikin mako mai zuwa, a cewar mai magana da yawun asibitin Cox's Bazar.
"Daman karshe" ga Aung San Suu Kyi
Zargi da kasashen duniya ke yi wa kasar Myanmar da murkushewa 'yan Rohingyas bai tsaya ga soja kawai ba, amma har kan Aung San Suu Kyi. Wacce ta samu lambar yabo ta Nobel ta yi shiru game da rikicin. A ranar Talata take so ta yi wani jawabin ."Ta na da daman karshe na [warware rikicin]", a cewar sakataren MDD Antonio Guterres.