1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rohani zai sayi jiragen sama a Faransa

Mouhamadou Awal BalarabeJanuary 27, 2016

A zango na biyu na ziyarar aiki da yake yi a wasu kasashen Turai, shugaban Iran Hassan Rohani ya nufin Faransa inda zai rattaba hannu a kan yarjeniyoyin cinikayya.

https://p.dw.com/p/1HkSi
Iran Präsident Hassan Rohani
Hoto: varzeshnews

Shugaba Hassan Rohani na Iran zai ya da zango a birnin Paris na Faransa a wani yunkuri na daidaita hulda da kasashen yammacin duniya da suka dage takunkunmin karya tattalin arziki da suka kakaba wa kasarsa. Dama dai ya shafe kwanaki biyu a Italiya inda ya gana da shugaban darikar Katolika ta Duniya Paparoma Francis da kuma mahukuntan kasar ta Italiya ciki kuwa har da Firaminista Mateo Renzi.

Rahoni zai iya amfani da wannan ziyara wajen rattaba hannu a kan wasu yarjejeniyoyin kasuwanci da takwaran aikinsa na Faransa Francois Hollande. Fadar mulki ta Teheran ta rigaya ta bayyana cewar za ta sayi jiragen sama 114 a Faransa. A kasar Italiya ma shugaban na Iran ya rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin cinikayya na miliyan dubu 17 na Euro.

A Ganawarsa da Paparoma Francis, shugaba Hassan Rohani ya taba rawar da Iran za ta iya takawa wajen dakile ayyukan ta'addanci a duniya tare da magance rikice-rikicen da suka addabi yankin Gabas ta Tsakiya.