Rodolfo Adada shugaban tawagar hadin gwiwa ta MDD da UA a Darfur | Labarai | DW | 08.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rodolfo Adada shugaban tawagar hadin gwiwa ta MDD da UA a Darfur

Majalisar Ɗinkin Dunia da ƙungiyar tarayya Afrika, sun zaɓi minsitan harakokin wajen ƙasar Kongo, Rodolfe Adada, a matsayin shugaban tawagar haɗin gwiwa ta ƙungiyoyin 2, a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Jmai´an na da yaunin jagorancin rundunar haɗin gwiwa da za ta gudanar da ayyukan tabatar da tsaro a wannan yanki da ke fama da tashe-tashen hankulla.

Wannan naɗi ya wakana a daidai lokacin da wakilin Majalisar Dinkin Dunia Jan Elliason, da na taraya Afrika Salim Ahmed Salim, su ka fara wani rangadi a yankin.