1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Roberts Gates ya ce dabarun yaƙin Amurka a Kandahar na tasiri

Ziyarar Sakataren tsaron Amurka a Sansanonin Amurka a Kandahar

default

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates ya bayyana cewar ya ga alamun da ke tabbatar da cewar dabarun Amurka a Afganistna yana yin tasiri a lardin Kandahar mai fama da rigingimu.

Gates ya yi wannan furucin ne bayan  rangadin sansanoni da ganawa da Dakarun Amurka a birnin na Kandahar da ke zama maɓuyan 'yan Taliban, kuma inda suke cigaba da yaƙar sojojin haɗakar.

Sakataren tsaron Amurkan ya kasa ɓoyewa 'yan jarida farin cikinsa a dangane da abun da ya kira Nasarar da dakarun Amurkan da na ƙungiyar tsaro ta NATO ke samu akan mayaƙan Taliban a fafatawar da ke gudana tsakanin ɓangarorin biyu a Kandahar. 

Mawallafiyya: Zainab Mohammad Abubakar

Edita:          Abdullahi Tanko Bala