Robert Zoellick zai hallarci taron sulhu na Abuja a game da rikicin Darfur | Labarai | DW | 01.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Robert Zoellick zai hallarci taron sulhu na Abuja a game da rikicin Darfur

A birnin Abuja na Taraya Nigeria, a na ci gaba da tantanawa, tsakanin tawagogin yan tawaye, da gwamnatin Sudan ,da zumar warware rikicin yankin Darfur.

Saidai, duk da kwanaki 2, da a ka ƙara, na wa´adin wannan tantanawa, akwai alamun ba za a cimma burin da a ka sa gaba ba.

A yau, shugaban tawagar gwamnatin Sudan, kuma maitamakin shugaban ƙasa, Ali Osman Mohamed Taha, ya fice daga zauren taron , zuwa Khartum, bayan ya zargi yan tawaye, da wasa da hankalin jama´a.

Yan tawayen yankin Darfur, sun yi tsaye kan bukatocin su, na samun kujera ɗaya, ta mataimakin shugaban ƙasa, a gwamnatin tarayya ta birnin Khartum,da kuma girka gwamnati a yankin Darfur, abinda hukumomin Sudan su ka ce, ba ta saɓuwa.

Amurika ta yi kira ga ɓangarorin 2, da su nuna halayen dattako, ta hanyar warware wannan rikici.

A yau gwamnartin Amurika, ta tura Robert Zoellick, mataimakin sakatariyar harakokin waje domin sa baki cikin wannan tantanawa.