Robert Zoellick: saban shugaban Bankin Dunia | Labarai | DW | 30.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Robert Zoellick: saban shugaban Bankin Dunia

Shugaba Georges Bush na Amurika, ya bayyana Robert Zoellick, a matsayin wanda zai gaji Paul Wolfowitz, a shugabancin Bankin Dunia.

Robert Zoellick ɗan shekaru 53 a dunia, ya riƙe manyan muƙamai a Amurika, wanda su ka haɗa da mataimakin sakataran harakokin waje, sannan ya wakilci Amurika,a kungiyar cinikaya ta dunia, wato WTO .

Wanda su ka yi aiki da shi , cikin tantanawar da ake, a ƙungiyar WTO, kokuma OMC, na yaba wa kyaukyawar aniyar sa, ta gannin an cimma masalaha, tsakanin ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki, da masu fama da talauci.

Bayan Amurika ta naɗa saban shugaban a hukunce,yanzu ya ragewa taron ƙoli, na ƙasashe membobin Bankin Dunia, su amince, ko kuma su yi watsi da wannan naɗi.

Idan su ka bayyana amicewa,ranar 1 ga watan juli Robert Zoellick zai fara jagorancin Bankin dunia.