1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Robbert Gates a Peru

October 6, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9F

A ziyararsa ta farko zuwa yankin Latin Amurka ,Sakataren tsaro na Amurka ya gana da shugaba Alan Garcia na Peru, adangane da matsalolin fataucin miyagun kwayoyi. Ministan tsaron kasar Allan Wagner yace,Gates da shugaba Garcia sun tattauna muhimman bangarorin da kasashen biyu zasu hada kai wajen yakar miyagun ayyuka,da suka hadar da miyagunkwayoyi da ake fataucinsu a yankin.Kazalika Sakataren tsaron Amurkan ya gana da shugaban kasar da sauran manyan jamian sojinsa,adangane da harkokin tsaro ,bayan rangadin daya kai kasashen Chile da Colombia da ElSalvador,ziyarar dake zama na farkon irinsa,tun daya maye gurbin Donald Rumsfeld a watan Disamba.