1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikita rikitar siyasar Faransa

March 23, 2010

A ƙasar Faransa an fara garanbawul ɗin ministoci, bayan mummunan kayen da Jam'iyar Sarkozy ta sha

https://p.dw.com/p/Ma3P
Nicolas SarkozyHoto: AP

Shugaban ƙasar Faransa Nicolas Sarkozy ya fara yiwa gwamnatinsa garanbawul, bayan mummunan kayen da jam'iyarsa tasha a zaɓen ƙananan hukumomin ƙasar da aka gudanar a arshen mako. Farkon wanda gyaran ta fara shafa shine ministan ƙwadugon ƙasar, bisa zargin da akayi masa na kasa gyaran tsarin biyan kuɗin fansho na ma'aikata asar. Ashirin daga ministocin gwamnatin Sarkozy suka tsaya takara a zaɓen ƙasar, kuma duk sun sha kaye. A halin da ake ciki kuwa ƙungiyoyin ƙwadugu a ƙasar sun shiga wani yajin aiki, inda suke adawa da rage ayyuka da kuma rashin jindaɗinsu bisa sabon tsarin  biyan fansho. Wannan yajin aikin zai katse zirga zirgan jiragen ƙasa, da sauran ayyukan makarantu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman  

Edita: Yahouza Sadissou Madobi