1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a kasar Gambiya

Lateefa Mustapha Ja'afar
January 19, 2017

Hankulan al'umomin kasa da kasa ya koma kasar Gambiya, a dai-dai lokacin da wa'adin shugaba Yahya Jammeh da ke kokarin yin kememe a kan mulki ke cika.

https://p.dw.com/p/2W34D
Al'ummar Gambiya na tserewa domin fargabar barkewar rikicin siyasa a kasar.
Al'ummar Gambiya na tserewa domin fargabar barkewar rikicin siyasa a kasar.Hoto: picture alliance / AP Photo

Hankula sun karkata zuwa kasar Gambiya sakamakon rikita-rikitar siyasar da kasar ke shirin tsintar kanta a ciki bayan da shugaban kasar mai barin gado Yahya Jammeh ya bayyana aniyarsa ta yin kememe akan gadon mulki, a dai-dai lokacin da wa'adn mulkin nasa ke cika. A hannu guda kuma shugaban kasar mai jiran gado Adama Barrow ya garzaya zuwa kasar Senegal, inda ake sa ran za a rantsar da shi a ofishin jakadancin Gambiya da ke Dakar babban birnin kasar.