1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikita-rikita tsakanin Turkiyya da Amirka

Yusuf Bala Nayaya
October 11, 2017

Turkiyya ta bayyana cewa ba za ta ci gaba da kallon jakadan Amirka a Ankra a matsayin wakilin kasar ba.

https://p.dw.com/p/2lcML
Symbolbild USA Türkei Beziehungen (Ausschnitt)
Hoto: Imago/imagebroker

Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana haka a ranar Talata abin da ke zuwa bayan kama wasu jami'ai da ke aiki a ofishin jakadancin na Amirka a Turkiya.

Heather Nauert da ke magana da yawun ofishin harkokin wajen Amirka ta ce ba su ji dadi ba kan yadda mahukuntan na Ankara suka kama jami'ai 'yan asalin Turkiyya da ke aiki a ofishin jakadancin na Amirka a birnin Santanbul, kuma ba a basu damar su yi magana da lauyoyinsu ba. 

"Ina ganin abin da ya kamata a fara da shi ne a bawa mutanen da aka kama dama su tattauna da lauyoyinsu, abin da muka sani kawo yanzu shi ne ba su da ikon yin hakan."

A ranar Lahadi ce dai Amirka ta tsayar da wasu harkoki da suka shafi bada visa a Turkiya saboda dalilai na tsaro, sa'oi kadan ita ma Turkiyya ta tsayar da bada visa ga wadanda ke dauke da fasfo na Amirka a ofishin jakadancinta da ke kasar ta Amirka.