1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin zaɓen shugaban ƙasa a kot-divuwar

November 4, 2010

Tsohon shugaban Kot divuwar ya ƙalubalanci sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da CENI ta wallafa.

https://p.dw.com/p/PxrU
Henri Konan BedieHoto: DW

Tsohon shugaban Kot divuwar wato Henri Konan Bedie da ya zo na uku a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana ranar lahadi ya zargi hukumar zaɓe da yi masa ƙwangen ƙuri'u. A lokacin da ya ke jawabi a birnin Abidjan bayan sanar da sakamakon zagayen farko na zaɓen shugaban ƙasa, Henri Konan Bedie mai shekaru 76 da haihuwa, ya bukaci hukumar ta sake ƙidaya ƙuri'un da aka kaɗa, saboda akwai ƙwararan shaidu da ke nuna cewar ta tafka kura-kurai a lokacin da ake ƙidaya ƙuri'un.

Sakamakon da shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanata wato Youssouf Bakayoko ya wallafa ya nunar da cewar za a fafata ne tsakanin shugaba mai barin gado, wato Laurent Gbagbo da kuma tsohon firaminista Alassane Ouatara a zagaye na biyu, da ka iya gudana a ranar 28 ga wannan wata na nowamba da muke ciki.

Shugaba Laurent Gbabgo ne ya zo na ɗaya sakamakaon lashe kashi 38,3% na ƙuri'un da aka kaɗa. Yayin da shi kuma tsohon firaminitan ƙasar ta Kot divuwar wato Alassane Ouatara ya ke biya masa baya da kashi 32 daga cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Umaru Aliyu