Rikicin yankin Palasdinawa | Labarai | DW | 01.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Palasdinawa

Acigaba da arangama tsakanin bangarori biyu dake adawa da juna a yankin palasdinawa,akalla mutane 4 ne suka rasa rayukansu a yau ayayinda wasu masu yawa suka jikkata a zirin Gaza.Wannan sabon rikici daya barke dai yana barazana wa yarjejeniyar da aka cimma na sulhu tsakaninsu,wanda ya shiga yini na uku ayau.Fadan daya gudana da bindigogi dai ya biyo bayan sace ayarin wasu jamiai ne da yan Hamas din sukayi, akan hanyarsu na kaiwa kayyakin masarufi wa dakarun Fatah.Majiyar yankin palasdinawan dai na nuni dacewa,yan biondiga dadin sun yi tsammanin cewa ayarin na dauke ne da makamai,dazaayi amfani dasu wajen kaiwa yan hamas din hari acigaba da wannan rikici nasu.