Rikicin yankin Naija Delta | Labarai | DW | 21.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Naija Delta

Rundunar sojin Najeriya tace sojojinta sun fattaki wasu yan bindiga da suka mamaye wani kanfanin mai mallakar kasar Italiya a yankin Naija Delta inda suka halaka mutane 12 tare da sako wasu yan Najeriya da akayi garkuwa da su.Tun ranar lahadi ake tsare da sojoji 11 da wasu kuma 27 a yankin,inda aka kashe akalla mutane 12 suka kuma sako wasu yan Najeriyar da akayi garkuwa da su.

Kakakin rundunar sojin a yankin Delta Manjo Omale Ochagwuba yace an dakarun sojin sun kori yan bindigar ne bayan fada da suka fafata tsakaninsu.

Mamayar da akayiwa yankin tun ranar lahadi ya tilastawa kanfanin mai na AGIP daya rage mai da yake hakowa da ganga dubu 37 a kowace rana.