Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 30.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya

Jiragen saman yakin Isra´ila sun tsananta hare haren da suke kaiwa a Zirin Gaza, inda a yau suka kai farmaki akan wurare guda 20 ciki har da ma´aikatar cikin gidan Falasdinawa, wadda suka yiwa kaca-kaca. Yayin da har yanzu dakarun kasa suna nan sun ja daga akan iyakar Zirin Gaza suna jiran umarni su kutsa cikin yankin. Rahotannin sun nunar da cewa Masar ta roka da a jinkirta ba da wannan umarni don ta samu karin lokacin shiga tsakani da nufin samun sakin sojin Isra´ila da Falasdinawa masu gwagwarmaya suka sace a ranar lahadi da ta gabata. Kungiyoyin Falasdinawa guda uku ciki har da bangaren soji na jam´iyar Hamas sun yi ikirarin sace sojan na Isra´ila. Babban sakataren MDD Kofi Annan da Amirka da KTT sun nuna damuwa game da kazancewar halin da ake ciki. Shi ma babban jami´in dake kula da taimakon jin kai na MDD Jan Egeland ya nuna damuwarsa da cewa fararen hula ne zasu fi shan wahala.