Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya | Labarai | DW | 07.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya

Kungiyar Hamas dake jagorantar gwamnatin Falasdinawa ta ce farmakin sojin da Isra´ila ta tsananta a Gaza ya kara dagula kokarin da ake yi na warware rikicin nan game da sojanta da aka sace kana kuma ya kara karfafa matsayin Falasdinawa game da makomar sojan. Wata sanarwa da Hamas ta bayar ta ce batun garkuwa da sojan ya kara dagulewa fiye da a da. A ci-gaba da hare haren da jiragen samanta ke kaiwa arewacin Gaza, Isra´ila ta sake kashe Falasdinawa biyu a yau juma´a, wanda hakan ya kawo yawan Falasdinawa da aka kashe tun bayan da Isra´ila ta tsananta hare hare a yankin a ranar laraba da daddare ya zuwa mutum 26. Isra´ila ta kaddamar da hare haren ne don matsa lamba a sako sojan ta da aka yi garkuwa da shi a ranar 25 ga watan yuni.