Rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya | Siyasa | DW | 21.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya

Kasar Iran na daga cikin kasashen da tilas a dama dasu a kokarin sasanta rikicin Yankin Gabas Ta Tsakiya

Daga cikin wadanda suka halarci taron a baya ga Mottaki har da shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai da P/M Pakistan Shaukat Aziz da Yerima Khalifa mai jirangado na kasar Bahrein da yerima Turki Al Faisal na Saudiyya da kuma P/M kasar Jordan Marouf Bakhit. Yerima Turki al Faisal, wanda yayi jakadancin kasarsa na tsawon shekaru a Amurka ya fara da gabatar da kira game da dakatar da zub da jini tsakanin Larabawa da kuma tsakanin Musulmi su ya su. Ya ce ana iya lura da wannan mummunan ci gaba a Irak da Lebanon da Afghanistan da Palasdinu. Wajibi ne a kawo karshen wannan babban abin kunya a cikin gaggawa. Shi kuwa P/M Pakistan Shaukat Aziz kira yayi da a nada wani kwamitin rikon kwarya da zai kunshi illahirin kasashen da rikicin yankin gabas ta tsakiyar ya shafa, saboda ta haka ne kawai za a kai ga warware rikicin. Iran dai na daga cikin kasashen da suka yi marhabin da wannan shawara kuma a shirye take ta taka muhimmiyar rawa wajen neman bakin zaren warware wadannan rikice-rikice. Wannan shi ne ainifin dalilin da ya sanya kasar ta amince da shiga taron da aka shirya gudanarwa tare da kasar Amurka akan kasar Iraki a ranar 28 ga wannan wata a matsayi na jakadu. Wannan ci gaba kuwa wani lamari ne na tarihi. Matsalar dake akwai tana da fuskoki ne guda biyu, a bangare guda akwai matsalar ta’addanci sannan a daya bangaren kuma akwai mamayar da Amurka ke wa Iraki. Wajibi ne a shawo kan dukkan matsalolin guda biyu, ta yadda dukkan sassan biyu wato Amurka da Iran zasu daina halayyarsu ta neman fakewa da guzuma domin su habi karsana. Dukkan Amurka da Iran dai babu daya daga cikinsu da tayi zaton cewar Iraki zata samu kanta a cikin irin wannan mummunan hali na zub da jini bayan kifar da mulkin Saddam hussein. Dangane da rikicin Isra’ila da Palasdinawa kuwa dukkan mahalarta taron na karshen baku sun dace akan cewar wajibi ne da farko a kawo karshen rashin jituwar da ake fama da ita yanzu haka tsakanin Palasdinawan su ya su kafin ayi batu a game da shawarwarin sulhu tare da Isra’ila akan sharadin mayarwa da larabawa yankunansu da Isra’ilar ta mamaye domin zaman lafiya da ita.