Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa | Labarai | DW | 14.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Gabas Ta Tsakiya tsakanin Isra´ila da Falasdinawa

Wani jirgin saman yakin Isra´ila ya harba rokoki 6 akanw ani gungun Palasdinawa a wani samame da sojin Isra´ila suka kai da asubahin yau a garin Jabalia dake Zirin Gaza. Rahotanni sun shaidar da cewa an halaka mutum 6 yayin da 9 suka jikata. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce dakarun Isra´ila a cikin tankokin yaki da motoci masu sulke da helikoftoci yaki sun kutsa cikin yankin Abed Rabbo dake gabashin garin na Jabalia a can arewacin Zirin na Gaza jim kadan bayan 12 dare. Gidan telebijin Isra´ila ya rawaito cewa an kai samamaen ne don hana harba rokoki daga Gaza zuwa cikin Isra´ila. A wani labarin kuma dakarun Isra´ila sun janye daga garin Abbassan bayan sun kashe Falasdinawa 7 ciki har da wani yaro da farar hula 2 bayan sun kwashe kwanaki biyu suna cin karensu babu babbaka a yankin na Falasdinawa.