Rikicin yankin gabas ta tsakiya sai gaba gaba yake.. | Labarai | DW | 08.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin gabas ta tsakiya sai gaba gaba yake..

A wani lokaci ne a nan gaba kadan a yau din nan tawagar kungiyyar kasashen larabawa zata isa Mdd, don bukatar gudanar da gyare gyare , a cikin daftarin neman yin sulhun rikicin yankin gabas ta tsakiya.

Kungiyyar dai ta kasashen larabawa ta yanke shawarar daukar wannan matakin ne bisa dalilin cewa daftarin ya gaza samar da shawarwarin daya kamata wajen kawo karshen wannan rikici.

Daftarin , wanda Amurka da Faransa suka tsara, har ila yau a cewar kungiyyar ta kasashen Larabawa ya gaza umartar dakarun sojin Israela dasu gaggauta ficewa daga kasar Lebanon.

A dai jiya litinin ne mahukuntan kasar Lebanon suka ce zasu tura tawagar soji dubu 15 izuwa kudancin kasar, don taimakawa dakarun Mdd tabbatar da tsaro da kuma oda.

A waje daya kuma, dakarun sojin Israela a daren jiya wato wayewar garin yau talata, sun yi ruwan bama bamai a kudancin birnin Beirut, wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwar mutane 8, a hannu daya kuma da jikkata wasu da dama.

A daya hannun kuma, rahotanni sun shaidar da cewa kungiyyar Hizboulla a jiya , sai da ta harba rokoki a kalla 160 izuwa arewacin kasar Israela, wanda hakan a cewar bayanai ya jikkata mutane uku.