Rikicin yankin Darfur | Labarai | DW | 13.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Darfur

Shugaban hukumar kulla da yan gudu hijira, ta Majalisar Dinkin Dunia, Antonio Guteres, ya bayyana kara gurbacewar zaman lahia a yankin Darfur na kasar Sudan.

A cikin wannan yanayi, ma´aikatan bada agaji na Majalisar Dinkin dunia ,da na kungiyoyi masu zaman kansu, na aiki jinni kan aikafa, ta la´akari da barazanar kissa, da su ke fuskanta a ko wane lokaci.

Hanya daya da ta cencenta a halinyanzu itace ta anfani da jiragen sama masu durra angulu domin kai agaji a wassu yankuna.

Antonio Guteres ya kira, ga komiti Sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, da ya kara basira ta fannin warware wannan rikici.

A wani rahoto ta ta fido jiya kungiyar kare hakokin bani Adama ta Human Rights Watch, ta zargi gwamnatin Soudan da babban lefi a cuikin ta´assar da ke wakana a yanki Darfur.