1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Darfur

April 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuNJ

Kasar Sudan tayi watsi da barazanar kakaba mata takunkumin karya tattalin arziki da ake yi, sabili da rikicin yankin darfur, abinda ta kira rashin adalci, ta kara da cewar zata yi iya kokarinta wajen ganin ta kare mutuncin kasar kana ta kara karfafa matakan tsaro. Kasashen Britaniya da Amurka sunce zasu gabatar da shawarar takunkumin bayan wani rahoto na amana da MDD ta gabatar wannan makon wanda ke zargin gwamnatin Kratoum da jigilar miyagun makamai zuwa yankin Darfur, duk da cewar yin hakan ya sabawa dokokin hukumar tsaro ta MDD. Ko da yake kasashen Russia, China da Afurka ta kudu sun bayyan adawa da wannan manufa, amma shugaban Amurka George W. Bush ya fada ranar laraba cewar kasar sa zata tsaurara matakan takunkumin karya tattalin arzikin kasa akan Sudan, idan har shugaba Omar al-Bashir bai dauki wasu kwarraran matakai na kawo karshen zub da jini da akeyi a yankin Darfur ba.