1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Darfur

June 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuJT

Shugaban ƙasar Sudan Omar Al Bashir ya maida martani, ga ƙudurin shugabanin ƙasashen G8, na bada goyan baya da kotun ƙasa ta ƙasa, ta Majalisar Ɗinkin Dunia, da ke buƙatar gurfanar da wani ministan ƙasar Sudan,da kuma shugaban ƙungiyar Janjawid, da ake zargi da hannu a cikin kissan gillar da ke wakana a yankin Darur na ƙasar Sudan.

Shugaban kotun majalisar Dinkin Dunia, Luis Moreno-Ocampo ya bukaci malajisar, ta yi iya kokarin ta, domin gurfanar da Harun Ahmed, ministan bada agaji na yanzu, da kuma shugaban Janjawid Ali Kosheib.

Sudan ta bayyana cewar kotunan ta na cikin gida, a shirye su ke, su zartar da hukucin da ya dace, ga mutanen 2, da zaran bincike ya tabbatar da hannu sun, a cikin wani lefi,a game da rikicin na Darfur.