Rikicin yankin Darfur | Labarai | DW | 25.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Darfur

Shugaban da zai jagoranci rundunar haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Dunia, da ƙungiyar taraya Afrika, a yankin Darfur na ƙasar Sudan, ya yi kira ga ƙasashe masu hannu da shuni, su tallafawa rundunar ƙungiyar gamayya Afrika, wadda a halin yanzu, ke gudanar da ayyukan kwantar da tarzoma a wannan yanki.

Rodolphe Adada, ya bayyana matsalolin da rundunar AU ke fuskanta, a dalili da rashin issasun kayan aiki.

Shugaban mai jiran gado, ya yayi hannun ka mai sanda, ga komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, wanda a yanzu haka, keci gaba, da mahaurori , a game da rundunar haɗin gwiwar.

Adada ya buƙaci baiwa wannan runduna cikkaken iko, na maida martani ko kuma na yin anfani da tsinin bindiga, domin ladabtar da yan tada zaune tsaye, a yankin Darfur.