Rikicin yankin Dafur. | Labarai | DW | 09.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin yankin Dafur.

Amurka ta ƙaddamar da wani sabon yunƙuri da zai ƙarfafa dakarun kiyaye zaman lafiya na ƙasa da ƙasa a lardin Dafur domin kawo ƙarshen taása da cin zarafin alúma a yankin. Shugaban Amurka George W Bush yace zai gabatar da buƙata ga kwamitin tsaro na MDD domin musanya dakarun gamaiyar Afrika dake Dafur da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya. Yana mai cewa alúmar Dafur na buƙatar tausayawa da kuma cikakkiyar kariya. Ya kuma baiyana agajin gaggawa ta dala miliyan 41.3 domin samar da gudunmawar abinci ga alúmar Sudan. A waje guda kuma jakadan kungiyar gamaiyar Afrika Salim Ahmed Salim yace akwai babban kalubale na aiwatar da yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin Gwamnatin Sudan da yan tawayen.