1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin ´yan tawayen Tamil Tigers a Sri Lanka

Sojojin ruwa na kasar Sri Lanka 15 aka kashe a wani harin kunar bakin wake da ake zargin ´yan tawayen Tamil Tigers da kaiwa. Kawo yanzu an gano gawawwakin sojojin ruwan 5 yayin da har yanzu ba´a guda 10 ba, wadanda ake kyautata zaton cewar su ma sun rigamu gidan gaskiya, bayan da wani kwalekwale da aka cika masa bama-bamai ya fashe lokacin da ya daki wani jirgin ruwan yaki. Hakan dai ya faru ne a daidai lokacin da ´yan tawayen na Tamil Tigers ke kara kai hare hare akan sojin kasar ta Sri Lanka. ´Yan tawayen sun yi barazanar komawa ga daukar makamai idan ba´a ba su ´yancin cin gashin kai ba.