1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ´yan kutse a Iraki

April 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1g

Wasu mutane da ba´a gane su ba sun farma wani caji ofis a birnin Bagadaza, inda suka kwashe sa´o´i da dama suna musayar wuta da jami´an tsaro. Wata sanarwa da hukuma ta bayar ta ce an kashe akalla mutum daya sannan da dama sun samu raunuka a gumurzun da aka yi a unguwar Adhamiya ta ´yan sunni. A halin da ake ciki sojoji sun yiwa unguwar kofar rago. A kuma halin da ake ciki babu wani ci-gaba a kokarin da ake yi kafa gwamnati a Iraqi watanni 4 bayan zaben ´yan majalisar dokoki. Bangaren ´yan shi´a sun ki a ba wakilin ´yan sunni Tarek el-Hashimi mukamin shugaban majalisar. Su kuma Kurdawa da ´yan Sunnin na adawa da kara wa´adin mulkin FM kuma dan Shi´a Ibrahim al-Jaafari.