Rikicin 'yan aware a Kamaru na yin kamari
June 12, 2018Talla
Kungiyar kare hakkin bil Adama ta duniya Amnesty International ta ce matakin amfani da karfin soji da gwamnatin Kamaru ke yi a yankuna biyu masu amfani da turancin Ingilishi a kasar Kamaru inda yan aware ke neman ballewa domin kafa 'yantacciyar kasarsu ya kara tagula lamura.
A wani rahoto mai shafi 37 da kungiyar ta Amnesty International ta wallafa, ta ce ta tattara bayanai na cin zarafi da rusa gidaje da kamen babu gaira babu dalili da kuma azabtarwa da jami'an tsaron Kamaru suka rika yi akan jama'a tun daga karshen 2017.
Kungiyar ta ce irin wannan mataki na kuntatawa ba zai magance matsalar ba.
Kawo yanzu yankunan da ke magana da harshen Ingilishi a Kamaru na da yawan jama'a kimanin miliyan 22.