1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin Xinjiang ya hana Hu zuwa taron G8

Illar rikicin kabilancin Sin akan taron G8

default

Shugaban Sin Hu Jintao


Shugaba Hu Jintao na ƙasar China, ya yanke ziyarar aikin da ya kai ƙasar Italiya, domin halartar taron man'yan ƙasashe takwas da suka ci gaba a fannin tattalin arziki, biyo bayan tashe tashen hankula na ƙabilancin daya ɓarke a yankin Xinjiang na ƙasar.

Ma'aikatar kula da harkokin wajen China, ta bayyana cewar, da sanyin safiyar wannan larabar ce, Shugaba Hu Jintao ya dawo gida China, saboda halin da ake ciki a yankin Xinjiang, inda a wannan talatar, wani sabon tashin hankali ya ɓarke a Urumqi, babban birnin yankin arewa maso yammacin ƙasar ta China. Dubbannin Sinawa 'yan Han - ɗauke da makamai ne dai ke yin jerin gwano a sassa daba daban na birnin Xinjiang, inda kimanin mutane ɗari ɗaya da hamsin da shidda suka rasa rayukansu a rikicin daya ɓarke a ƙarshen makon daya gabata.

Uiguren / Xinjiang

Xinjiang

Duk da cewar China bata cikin jerin ƙasashen dake da ƙarfin tattalin aziki na G8, amma an gayyaceta zuwa taron, domin mafi yawan batutuwan da taron zai taɓo, sun haɗa dana ƙasashen da tattalin arzikinsu ke haɓaka.

Farfesa Jean - Pierre Cabestan, masanin kimiyyar siyasa dake jami'ar Hong Kong ya ce katse ziyarar da shugaba Hu ya yi, wata alamar nuna damuwa da kaɗuwa ne bisa abubuwan dake faruwa a yankin.

Wani tsohon ma'aikacin dake zaune a yankin kuwa cewa ya yi:

" Ni tsohon ma'aikacin dake karɓar Fansho ne, ba ni da masaniya dangane da wannan rikicin."

Shi kuwa wannan mutumin da aka yi hira dashi, cewa yake:

" Ni, a telebijin ne na gani. Banyi zurfin tunani dangane da rikicin ba, domin rikicin bai shafi rayuwata sosai ba. Don haka, bani da abinda zan ce. A ganina gwamnatin na yin iyakar ƙoƙarinta na shawo kan matsalar. A tsawon lokaci, kowa ya san cewar, Xinjing wuri ne na zaman lafiya. Akan samu tashe tashen hankula a kowane gari, kuma na san komai zai daidaita."

Wani ɗan kasuwar daya taho daga Shanhai kuwa cewa ya yi matsalar ta shafi harkar kasuwancinsa:

" Na dakatar da harkokin kasuwanci na sakamakon rikicin na Xinjiang. Na kanyi sayayyata anan. Daga Shanhai, muna da kyakkyawan yanayin sufuri zuwa Xinjing . Mafi yawan mazauna Shanhai suna aiki a can. Abinda ke faruwa yanzu, batu ne na tarzoma, wanda ke da alaƙa da ƙungiyoyin ƙetare"

Uiguren / Xinjiang

Xinjiang

Tashin hankalin daya sake ɓarkewa a yankin Xinjiang a yammacin talata dai, ya zo ne a matsayin mayar da martani ga rikicin daya faru kwanaki biyu - gabannin hakan, inda dubbannin al'ummar Uighur, waɗanda galibinsu musulmai suka gudanar da zanga zangar da tayi sanadiyyar wasu mutane, a yayin d kimanin wasu mutane dubu kuma, suka sami rauni.

Kafin katse ziyararsa a ƙasar Italiya dai, a ranar litinin ne shugaba Hu ya gana da takwar aikinsa na Italiya Giorgio Napolitano da kuma Frime minista Silvio Berlzsconi.

Bayan tada batun haƙƙin jama'a tare da Hu, Napolitano ya shaidawa taron manema labarai na haɗin gwiwa cewar, sun sami daidaito kan cewar, ci gaban tattalin arziki dana rayuwar a China, kamata ya yi a bisu da kyautata mutunta haƙƙin bil'adama.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Zainab Mohammed