1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

RIKICIN WARWARE MATSALAR KAURA A JAMUS DA NAHIYAR TURAI.

Har ila yau dai, ana ta ci gaba da muhawara kan shawarar nan da ministan harkokin cikin gidan Jamus, Otto Schilly ya gabatar, na fara jibge makaurata zuwa Turai, a arewacin Afirka, kafin a ji koke-koken da suke tafe da shi. Akwai dai masharhanta da dama da suke adawa da wannan ra'ayin.

Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Jamus, Otto Schilly.

Ministan harkokin cikin gida na tarayyar Jamus, Otto Schilly.

Duk wanda ya yi kokarin fahimtar ministan harkokin cikin gidan Jamus Otto Schilly dai, zai gano cewa, dabararsa ce tura matsalolin da ke kunno kai nesa da shi, yana mai zaton cewa idan ya yi hakan, to matsalolin za su warware kansu da kansu. Da wannan salon ne kuwa, yake yunkurin shawo kan takwarorinsa na kungiyar Hadin Kan Turai, da su goyi bayan ra’ayin da ya gabatar na kafa sansanin tara maneman mafaka da ke niyyar shigowa kasashen kungiyar, a arewacin Afirka.

Bisa lissafin da ministan ke yi dai, idan hakan ya samu, to sam ma ba za a sami maneman mafaka a nan Jamus ba. Saboda kafin wani bako ya zo nan kasar neman mafaka ma, tuni a tare shi a kan hanyarsa, an jibge shi a wani sansani, a wata kasa daban. A lal misali, makaurata daga Tajikistan ko Moldaviya, za a iya jibge su ne a kasar Ukraine, saboda ba za su iya tsallake iyakokin kasashen gabashin turan da suka shigo cikin kungiyar Hadin Kan Turan ba kuma, kamar yadda suke yi a da. Amma a kudancin Turai, lamarin daban yake. Hanyar ruwan da ke tsakanin gabar tekun nahiyar Afirka da iyakar kudancin Turai ba ta tsaruwa. Duk tsauraran matakan da ake dauka, ba sa hana bakin haure yunkurin tsallake tekun bahar rum da kwalekwale ko kuma kananan jiragen ruwa, don su sami shiga nahiyar Turan ta kasar Spain, ko Italiya ko kuma Girka. Sabili da haka ne dai, Otto Schilly, ya kago wannan shawarar, ta kafa sansanin tara makauratan ko a kasar Marokko, ko Tunesiya ko kuma Libiya, kafin ma su nemi hanyar tsallake tekun na bahar rum.

Babu shakka, ra’ayin ministan na da wasu fa’idoji. Amma babu wadanda za su fi gamsuwa da shi kamar masu tsatsaurar ra’ayi. Ta hakan ne kuwa, za su iya yada ra’ayin mai da duk baki abin tsoro a nan kasar.

Tun ba a fara aiwatad da wannan matakin ba ma, ai an gano cewa yawan maneman mafaka a na Jamus sai kara raguwa yake yi. Alkaluma na nuna cewa, a cikin wannan shekarar da kuma shekarar bara, yawan maneman mafaka a nan Jamus ya ragu da kashi daya bisa uku. A halin yanzu kam, yawan duk maneman mafakar da ke nan Jamus bai fi miliyan daya da `yan kai ba. Gaba daya kuma, yawan baki da ke zaune a nan Jamus ya kai miliyan 7. Mafi yawan wadannan kuwa, ma’aikata ne da ke biyan haraji da kudaden fansho. Kafofin kula da jin dadin jama’ar nan kasar dai sun dogara a ne galibi, kan kudaden da bakin ke biya cikin asusun fanshon da dai sauransu.

Wajibi ne dai, a bayyana wadannan alkaluman, don yin gyara ga rade-radin da ke ta yaduwa na cewar, ai dimbin yawan bakin haure daga nahiyar Afirka, ko kuma marasa galihu daga gabshin Turai ne ke ta shigowa nan Jamus. A zahiri ba haka lamarin yake ba. Mafi yawan `yan gudun hijiran daga nahiyar Afirka, ba a nan Tturai suke ba. A can cikin nahiyar suke. Idan aka dubi alkaluman yawan `yan gudun hijira a nahiyar Afirka za a ga cewa, mafi yawansu a kasashe kamarsu Kwango suke, ko kuma a yankunan manyan tafkunan nan na gabshin Afirka, ko kuma a Somaliya. A wadannan yankunan ko kuma kasashen, akwai dimbin yawan `yan gudun hijira, wadanda ba a san da su ba ma a nan Turai.

Ra’ayin da Otto Schilly ke gabatarwa kuwa, wato na kafa sansanin tara maneman mafakan a arewacin Afirka, a tantance su tukuna, kafin a tsai da shawarar amincewa da bukatunsu ko kuma yin watsi da su, ba kome ba ne illa kikiro wata kafa, wadda za ta iya yin yadda ta ga dama da `yan gudun hijiran, ba tare da bin wasu ka’idojin kare hakkin dan Adam ba. Tuni dai ministan ya bayyana cewa, a wadannan sansanonin, ba za a yi amfani da ka’idojin da shari’a ta ajiye na jin kararrakin maneman mafaka a nahiyar Turai ba. Wato ke nan a zahiri, kungiyar Hadin Kan Turan, ba sha’awar ganin an warware matsalar `yan gudun hijiran take yi ba. Gurinta ne ta tura matsalolin can nesa da ita, ba tare da ta nemi warware su ba. Har ila yau dai, a tattaunawar da suke ta yi a birnin Brussels, ministocin harkokin cikin gida na kungiyar Hadin Kan Turan, sun gaza cim ma daidaito na bai daya, game da yadda za su tinkari wannan matsalar ta `yan gudun hijira, a huskar shari’a. A nan Jamus kuma, har ila yau, ba a cim ma wata manufa ta kayyade batun nan na kaura, wadda za ta yi la’akari da kalubalen da ake huskanta a fannonin yawan jama’a da kuma tattalin arziki ba tukuna.

Kamata ya yi dai, `yan siyasa a nan nahiyar Turai, su san cewa, a galibi su ne ummal aba’isin matsalolin da ke kunno musu kai a ko yaushe, ta kin nuna sha’awa ko damuwa ga matslolin da ke ci wa makwabtansu tuwo a kwarya.

 • Kwanan wata 06.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhV
 • Kwanan wata 06.08.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvhV