1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Ukrain

Babu alamun cewa zaa warware takaddamar siyasa data barke a kasar Ukraine nan kusa.Bayan taron majalisar tsaron kasar a birnin Kiev,shugaba Vicktor Yushchenko dake da goyon bayan shugabannin kasashen yammaci ,yayi barazanar gurfanar da dukkan wani maaikacin gwamnatin daya sabawa dokarsa ta gudanar da zabe cikin gaggawa.Ayayinda prime minista Vicktor Yanucovych ya fadawa yan majalisarsa cewa ,kada su yarda su shiga wannan zabe,har sai kotun tsarin mulkin kasar ta tantance sahihancin wannan doka ta shugaban kasa.Bugu da kari ya kumayi kira ga shugaban gwamnatin Austria Alfred GUsenbauer,daya shiga tsakani wajen shawo kann wannan matsala ta siyasa da ukraine din ta tsinci kanta ciki.