1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

190510 Thailand Zuspitzung

May 19, 2010

Sojoji a Thailand sun fara aikin kawar da masu bore dake adawa da gwamnatin ƙasar mai samun goyon bayan soji

https://p.dw.com/p/NRdC
Wuta na ci a BangkockHoto: AP

Sojoji a birnin Bangkok babban birnin ƙasar Thailand, sun fara ragargaza shingayen da masu adawa da gwamnati suka fa, inda suke ta harbin duk wani da suka samu. Gwamnatin ƙasar ta tasanma hakanne bayan da tace babu wata tattaunawa da za ta yi da masu zanga zangar, illah kwai ayi anfani da ƙarfi don kawar dasu. Usman Shehu Usman ya duba mana halin da ƙasar ke ciki.

Tun a sanyin safiyar yaune dai sojoji tafe da motocin sulke da buldoza, suka fara yin raga raga da shingayen da masu adawa da gwamnatin. Inda kuma suka fara buɗe wuta ta ko ina a yankin da masu zangara suka yi sansani a tsakiyar birnin Bangkock.

Ta ko ina dai harbi kawai ka ke ji. su ma masu boren suna cilla wuta daga sansanin da suka kame.

Kafin dai akai ga wannan sanda gwamnatin ƙasar ta fitar da wata sanarwa mai kama da gargarɗi, kamar yadda kakakin gwamnatin ƙasar Panita Wattanayagorn ya yi wa al'ummar ƙasar jawabi,

"Maza da mata, gwamnati tana son shaida muku cewa, samar da tsaro a wuraren da aka killace cikin Bangkock ya samu nassara. Muna so mu shaida muku cewa akwai bataliyoyin tsaro dake biye da sojojin. Muna fatan za ku ba mu goyon baya, don samun murƙushe wannnan tarzomar. Muna godiya da neman haɗin kanku."

Aƙalla mutane dubu bakawai ke zama a anguwar da tashin hankalin ya fi ƙamari, a sabili da wannan tashin hankali kusan dukkanninsu sun bar gidajensu, inda waɗansu ke kwana a makarantu.

A yayin da lamarin yayi ƙamari a yau, masu boren sun yi ta bankawa gidajen mai wuta da ƙona tayoyi dama banka wuta ga babbar sakatariyar gwamnati ta biyu mafi girma a babban birnin ƙasar wato Bangkok, da duk wani abinda suka san zai iya kama wuta domin hana sojin cimmusu.

Yanzu dai masu boren sun kafa wasu sabbin sansanoni, inda dubun dubatansu ke neman kayan kare kai. Su dai masu zanga zangar dake sanye da jajayen riguna, suna buƙatar lallai sai a sauke gwamnati wanda soji ke marawa baya, kana a gudanar da zaɓe. Ita kuwa gwamnatin Thailand ta ce babu wata tattaunawa da za ta yi da mutanen, har sai an kawar da duk wani shinge.

Masu aiko da rohotonni suka ce aƙalla mutane 40 suka rasa rayukansu tun ranar da Alhamis da aka fara yunƙurin tarwatsa masu boren, inda kuma idan aka yi lissafi tun watanni biyu da aka fara zanga zangar, to kimanin mutane 60 suka mutu wasu a ƙalla dubu ɗaya suka jikkata.

Mawallafa: Usman Shehu Usman da Bernd Musch-Borowska,

Edita: Muhammad Nasiru Awal