1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shin ko shugaba Tanja Mammadu na Nijar zashi tazarce ?

March 29, 2009

Rikicin tazarce a Nijar:" Idan kaga kare na sinsinar takalmi ƙarshen ta ya ɗauka"

https://p.dw.com/p/HMKR
Ko Tanja Mammadu zai zarcewa ?Hoto: AP Photo


Shugaban Jamhuriya Nijar Tanja Mamadou,a karon farko ya bayyana matsayinsa a game da cecekucen da ake tafkawa akan batun tazarce.

Shirin duniya mai yayi a wannan karo, zai sake duba halin da ake ciki a Jamhuriya Niger, akan wannan batu wanda ke cigaba da ɗaukar hankalin ´yan siyasa.

Ranar juma´a 27 ga watan Maris na shekara ta 2009, shugaban ƙasar France Nikolas Sarkozy ya kai rangadin farko a Jamhuriya Niger, inda ya tattana da takwaransa Tanja Mamadou, a game da batutuwa dabam dabam da suka shafi cinikiyya, da kuma mu´amila tsakanin ƙasashensu biyu.

A ƙarshen ganawar ƙut da ƙut, shugabanin sun shirya taron manema labarai na haɗin gwiwa.

Babban batun da ya fi ɗaukar hankalin ´yan jarida shine na tazarce.

A karon farko,shugaba Tanja Mammadou ya fasa ƙwai.Ya bayyana matsayinsa tare da cewa:

Al´umar Niger ta jima tana jiran hurucin shugaba Tanja Mamadou a game da batun tazarcen, to saidai kalamomin da yayi sun ƙara sa ruɗami , domin ra´ayoyin jama´a sun bambanta, a yayin da wasu ke tunanin shugaban zai sauka, wasun kuma ga ganin akasin haka.

Alhaji Adamou Mahaman Madaoua, ɗan Niger ne dake zaune a Nigeria, kuma jagoran masu neman tazarce, na tuntuɓe shi a cikin shirin ,inda na tambaye shi fassara da yayiwa jawabin shugaba tanja Mamadou.

A cikin kalamomin da yayi a lokacin taron mema labari da shugaba Nikolas Sarkozy ,Tanja Mamadou, yace a shirye yake ya sauka daga karagar mulki ranar 22 ga watan Desember na shekara ta 2009, dake matsayin ƙarshen wa´adin mulkinsa, to saidai a game da buƙatar wasu ´yan ƙasa ta ya zarce, magana ta ragewa jama´ar ƙasa da Majalisar Dokoki.

A game da haka, Alhaji Adamu Mahaman Madawa yayi kira ga ´yan majalisa da suka dauki matakan da suka dace dominTanja Mamadou yayi tazarce.

A nasu gefe, Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin demokraɗiya sunce basu yi mamakin bayyani shugaba Tanja Mamadou ba, kuma kamar yadda malam bahaushe ke faɗi "idan kaga kare na sisinar takalami, ƙarshen ta ya ɗauka".

A cewar Tsayabu Lawal Salaou, shugaban haɗin gwiwar Ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani adama da demokraɗiya a Niger wato Roddahd, doka bata baiwa Majalisar dokoki ikon sa shugaban ƙasa yayi tazarce ba

A halin da ake ci dai yanzu, mahaura ta kabre a fagen siyasar, inda kowa ke tsokaci agame da batun na tazarce,Abdu Umaru,shine mataimakin shugaban jam´iyar PNA Al´uma mai adawa,ya bayyana ra´ayinsa tare da cewa:

Tun a watanin baya, jihohi dabam-dabam na Jamhuriya Niger sun shirya tafiyoyin jerin gwano na neman shugaba Tanja Mamadou yayi.

Masu fafatar cimma wannan burin sun ƙara samun ƙarfin gwiwa wajen shugaban kasa Libiya bugu da kari shugaban kungiyar tarayya Afrika Mohammar Khaddafi.

To saidai Ƙungiyoyin fara hulla sunce sam, tazarce ba zata zartu ba,kamar yadda shugabankungiyar Roddadh ya nunar:

Yanzu dai hankulla jama´ar Niger sun karkata, wajen hukumar zaɓe mai zaman kanta wato CENI ,da aka girka makon da ya gabata, mussamman domin ganin tsarin ranekun zaɓɓuɓuka da zata gabatar.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Abdullahi Tanko Bala