Rikicin tawaye a Philipines | Labarai | DW | 20.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a Philipines

Kasar Phillipines ta sha alwashin cewar zata kara karfafa matakai na kawo karshen ‘yan yakin sunkuru, yayin da take mayar da martani akan wani harin da wani reshe na al-Qaida na Abu Sayyaf ya kai, tare fylle kannun wasu kiristoci bakwai da aka yi garkuwa da su, a jiya alhamis, daga baya dakarun suka aika da kannun ta hannun wasu farar hulla zuwa tsibirin Jalo inda ake fama da tashe tashen hankula. Shugaba Gloria Arroya tace wannan danyen aikin na fylle kannun mutane na nuna rashin imani daga kungiyar ta Abu Sayyaf.