Rikicin tawaye a Niger
July 10, 2007Talla
Ƙungiyar yan tawayen MNJ a Jamhuriya Niger, ta bayyana aniyar sakin ɗan kasar Sin ɗin nan, da ta yi garkuwa da shi, tun ranar juma´a da ta wuce.
Shugaban ƙungiyar, Aghali Allambo, ya bayyanawa kampanin dullancin labaran Reuters wannan labari.
A cewar Aghali Allambo , nan bada jimawa ba za su mika Zhang Guohua ga hukumar bada agaji da Croix Rouge kokuma Red Cross.
Ƙungiyar tawayen MNJ da ke ci gaba da kai hare-hare a yankin Agadaz mai arzikin ƙarƙashin ƙasa a Jamhuriya Niger, ta yi gargaɗi ga kampanonin ƙasashen ƙetare, masu ayyukan binciken ma´adanai, da su fice daga wannan yanki.