1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a Mali

Ministan tsaron ƙasar Mali ya bayyana sanarwa a game da halin da ake ciki a rikicin tawayen da ke wakana a wannan ƙasa.

Sanarwar ta nunar da cewa yan tawayen sun ranta cikin na kare, a sakamakon ƙarin ƙarfin da rundunar sojoji ta samu, a yankin da ke fama da tashe-tashen hankula.

Yan tawayen a cewar ministan tsaron ƙasar Mali, sun ƙetara iyaka zuwa ƙasar Algeria.

Sanarwar ta kara da cewa a yanzu yankin Tinza da yan tawayen na Ibrahim Bahanga su ka mamaye, ya dawo cikin hannun sojojin gwamnati, wanda ke ci gaba da tone nakiyoyin ƙarƙashin ƙasa da yan tawayen su ka bunne.