Rikicin tawaye a kasar Kote Divoire | Siyasa | DW | 02.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin tawaye a kasar Kote Divoire

Shugaban rundunar shiga tsakani ta Majalisar DinkinDunia a kasar Cote Divoire, ya gana da shuwagabanin rundunar yan tayawe, da kuma shugaban habsan habsoshin sojoji masu biyaya ga gwamnati.

Babban burin da ke tattare da wannan tarruruka, shine na neman hanyoyin warware sabuwar damabarwar siyasar da ta kunno kai a kasar.

Idan ba a manta ba, a satin da ya wuce, yan tawaye, da yan adawa su ka bayana aniyar su, ta kauracewa zaben shugaban kasa,da a ka tanadi yi, ranar 30 ga watan okober mai zuwa, sannan a daya gefen, su ka bukaci girka sabuwar gwamnatin rikwan kwarya, daga ranar ta 30 ga watan oktober, da a cewar su, a rannan ne, shugaba mai ci yanzu, Lauran Bagbo ke kai wa´adin karashe, a karagar mulki.

Sannan a ware Lauran Bagbo, a cikin gwamnatin da za a kaffa.

Al´ammura sun dadda dagulewa, bayan da yan tawaye su ka bayana watsi, da shiga tsakanin shugaban Afrika ta Kudu,Tabon Mbeki, da su ka zarga, da nuna san rai, ta hanyar nuna fifiko ga bangaren Lauran Bagbo.

Don dinke wannan sabuwar baraka, da kuma kussanto da ra´ayoyi daban daban, na yan siyasa, da yan tawaye, shugaban rundunar shiga tsakani, ta Majalisar Dinkin Dunia, Jannar Fernand Amussu, ya gana da farko da shugaban rundunar sojoji masu biyyaya ga gwamnati,Jannar Fillip Mangu, a birninn Yamuskuro.

A ganawar da yayi, da shugaban rundunar tawayen FN ,Jannar Amussu, ya tantanna, da takwaran sa, Jannar Sumaila Bakayoko, a kan mahiman batutuwa da su ka jibanci, samar da zaman lahia, a duk fadin kasar Cote Divoire , mussamman a yankin iyaka, dake matsayin sasannin dakarun Majalisar Dinkin Dunia.

A ranar laraba da ta wuce, tawagar shiga tsakanin, ta rasa daya daga sojojin ta.

A daya hannun, kuma,tawagogin 2, sun yi masanyar ra´ayoyi, a game da batun tsaro, a lokacin da za a jarabawar karshen shekara ta yan makaranta, a watan damu ke ciki, a yankin arewancin kasar da ke hannun yan tawaye.

Bangarorin 2, sun amince su gama karfi, don cimma wannan buri.

Ministan tsaro ta kasar Fransa, Mishel Alio Marie ta jaddada kira ga bangarori masu gaba da juna, a kasar Kote Divoire, da su koma tebrin shawara, domin sake kulla zaren tantanawa da ya katse.Ta kuma bukaci Majalisar Dinkin Dunia, ta kara zage dantse, a fadi ka tashin da ta ke na warware rikicin Kote Divoire.

A dangane da batun zabe, da ya jawo cecekuce, Mishel Alio Marie, ta gayyaci wakilin mussaman na Koffi Annan, a kasar KOte Divoire, Antonio Monteiro, da ya bayanawa majalisar zahirin maiyiwuwa.

Majalisar r ked a hakin yanke hukuncin dagewa da shirya zabe a ranar ta 30 ga watan oktober.

Ministan , ta jaddada goyan baya, Tabon Mbeki da ke shiga tsakani a wanann rikici.

Saidai masu kulla da harakokin siyasa a kasar, na hasashen cewa abun da kamar wuya Tabon Mbeki ya ci gaba da wannan aiki idan aka dubi rashin yarda da ya shiga tsakanin sa da yan tawaye.

 • Kwanan wata 02.09.2005
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZw
 • Kwanan wata 02.09.2005
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZw