1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin tawaye a Cote d´Ivoire ya dauki saban sallo

Yahouza sadissouAugust 26, 2005

Yan tawayen FN a Kasar Cote d´Ivoire sun yanke shawara kauracewa zaben shugaban kasa na 30 ga watan oktoba

https://p.dw.com/p/BvaA

A karshen taron da su ka fara, tun ranar 17 ga watan da mu ke ciki, shugabanin kungiyar tawaye, ta FN a kasar Cote d´Ivoire, wanda a yanzu haka, ke rike da arewancin kasar, sun bayyana aniyar su, ta kauracewa zaben shugaban kasa, da za a yi ranar 30 ga watan oktoba.

Yan tawayen, su yanke wannan shawara, domin a cewar su, a halin da ke ciki, babu mattakan da aka dauka,kokuma babu alamun za a daukar su, na tabbatar da shirya zaben cikin adalci.

Sanarawar da su ka fido,a karshen taron, ta bayyana cewa, ba zata yiwu ba, a shirya wanan zabe cikin kyawkyawan yanayi, muddun shugaba Lauran Bagbo,na kan kujera mulki, domin shine ke dabaibaye samar da zaman lahia, da kuma cimma matakan sulhu daban daban da bangarori masu gaba da juna su ka cimma, bayan mahaurori na dogon lokaci.

Yan tawayen FN, sun sanar cewa, ranar 30 ne ga watan oktoba wa´adin mulkin Lauran bagbo ke kai karshe.

Daga wannan rana, ya kare zama shugaban kasar Cote d´Ivoire, a idon yan tawaye, a game da haka, wajibi ne ya kaw ya bar wuri, ga wata sabuwar gwamnatin rikon kwarya.

Yan tawayen, sun shawarci jam´iyu siyasa, da su kiri taro na musamman, wanda zai shata ka´idoji, da sharrudan saban mulkin rikon kwaryar.

Sanarwar da kungiyar FN ta hido ta gargadi Lauran bagbo, da ya yi shirin barin kujera mulki, cikin an dadde ranar 30 ga watan oktoba a shabiyun dare, idan wa´adin ya wuce, ya kuma ci gaba da dawwama bisa karaga mulki, to dukan abin da ya biwo baya, shine sanadiya, domin kuwa, rundunar tawaye ta daura shirin ko takwan, domin ganin ta ko wace hanya, ta dasa aya ga shugabancin Bagbo.

A daya hannun, sanarwar ta bayana amincewar yan tawaye na shiga a dama da su, a hukumar zabe mai zaman kanta.

Saidai, a nan ma sun gitta sharuda, da su hada da watsi da dokar da Bagbo ya sa ma hannu, a watan da ya gabata, da kuma tsame hannu hukumar rijista ta kasa daga al ammuran zabe.

Daga cikin hanyoyin da yan tawaye su ka bada shawara ,na tsara zabe, mai tsabta, akwai da farko rijistan yan kasa ta hanayar adalci a dukkna jihohi, sannamataki na 2 shine na rijistan mutanen da ya cencenta su kada kuri´u sanna daga karshe tanadar matakan tsaro masu inganci da za su baiwa dukan masu zabe damar kada kuriun su ba tare da fuskantar barazana ba.

Wanan sananarwa da yan taawye su ka fido ta biwo bayaan kalamomin tsofan shugaban rundunar tsaro ta kasa inda ya bayaan aniyar s ata kiffar da shugaba Lauran Bagbo.

A halin da ake ciki al´ummar ta shiga cikin wani saban hali na rudani.

A game da haka shugaban rundunar sojoji masu biyyaya ga gwamnati, yayi kira ga jama´a,da ta kwantar da hankali, ya kuma tabatar da cewa, rundunar sa, na tsaye tsayin daka, domin kariyar lahia su.

Dalili da wannan gurbatacen yanayi, Amurika ta yi kira ga yan assalinta, dake Cote d´Ivoire, da su shirya ficewa daga wannan kasa, muddun kasancewar su a ciki ba ta zama ba cilas, sannan dukan masu bukatar zuwa da bullaguro su yi takatsatsan.