Rikicin tawaye a ƙasar mali | Labarai | DW | 23.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin tawaye a ƙasar mali

Rahotani daga ƙasar Mali ,sun ce wasu mutane ɗauke da makamai, da ake dangatawa da yan tawaye, sun kai hare hare, ga wasu sansanonin soja, da ke birnin Kidal a arewa maso gabacin ƙasar.

A halin da ake ciki, yan tawayen ke riƙe da wannan sasanoni, bayan sun kame da dama, da ga sojoji gwamnati, a yayin da wasun kuma, su ka ranta cikin na kare.

Saidai babu cikkaken bayani, na yawan mutanen da su ka rasa rayuka.

Ƙasar Mali, na ɗaya daga ƙasashen Afrika, da su ka fuskancin matsalolin tawaye.

Saidai, a shekara ta 1996, da a ka rataba hannu a kan yarjejeniyar zaman lahia, tsakanin Gwamnati da yan tawayen.

A sakamakon hakan, gwamnati ta ɗauki, wasu daga tsaffin yan tawayen, a ciki rundunonin tsaro na ƙasa.

Amma a baya bayan nan, da dama, daga cikin su,suka yi murabus.

Shugaban rundunar tsaro, ta birnin Meneka da ke gabanci ƙasar,da kansa, ya jagorancin ayarin yan tawaye ,da su ka kwashe makaman rundunnar, domin kai hari, ga jamai´an tsaron wannan yanki, wanda a halin yanzu ke cikin hannun su.