1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

280410 Reaktionen Griechenland

April 28, 2010

Girika ba ta da ƙarfin biyan basussukan da take son ciyowa

https://p.dw.com/p/N8pQ
Ministan kuɗin Girika Giorgos PapaconstantinouHoto: AP

Hukumar nan dake ƙimanta darajar ƙasashe a fannin tattalin arziki wato Standard and Poor's ta rage ƙarfin biyan bashin ƙasar Girika zuwa matsayi na ƙarshe. Wannan ƙiyasin ya sake haddasa rashin sanin tabbas a kasuwannin hada-hadar kuɗi. Sai dai da sanyin safiyar Larabar nan yawan kuɗaɗen ajiyarta na tsawon shekaru biyu, ya tashi da misalin kashi 25 cikin 100. A saboda haka a ƙasar ta Girika aka nuna rashin amincewa da ƙiyasin.

Dukkan kafafan yaɗa labarun ƙasar Girika sun yi ta yin kira ne da a nuna juriya. Kakakin gwamnati Giorgos Petalotis ya yi ƙoƙarin kwantar da hankula yana mai cewa.

"Kuɗaɗen ajiyarmu suna nan daram. Tsarin tafiyar da bankuna a Girika suna nan lafiya lau. Duk ko menene wasu za su faɗa, ƙasarmu kam tana tsaye daram."

Ga Petalotis babu wani bayani dangane da ƙididdigar da hukumar Standard and Poor's mai ƙimanta darajar ƙasashe a fannin tattalin arziki ta yi amfani da ita wajen yanke wannan hukunci cewa hannayen jarin ƙasar ta Girika ba su da wata daraja yanzu.

Shi ma ministan kuɗin Girika Giorgos Papa-Constantinou ya ce ƙiyasin ba daidai ba ne. Hasali tattaunawar da suke da Asusun Ba da Lamuni na ƙasa da ƙasa IMF da ƙungiyar Tarayyar Turai EU, ta doshi hanyar cimma nasara.

"Muna sauraran dukkan ra'ayoyi da ke fitowa nan da can musamman a ƙasar Jamus."

Ministan ya fito ƙarara ya ambaci sunan Jamus yana mai nuni da shakkun da 'yan siyasar Jamus ke nunawa cewa ko lalle ya kamata a taimakawa Girika ko kuma a'a. Ministan ya ce wannan shi ke kawo tsaiko wajen cimma matsaya da wuri a tattaunawar.

Bai kamata mu sake ɓata lokaci ba. Muna cikin kyakkyawar tattaunawa game da matakan da za mu iya aiwatarwa da shirin tsimi da za mu gabatar a cikin shekaru uku masu zuwa."

Ministan ya yi fatan cewa za a cimma yarjejeniya kan ba da taimakon kuɗin

sannan a cikin kwanaki biyu ko uku masu zuwa a gabatar da shirin tsimin kuɗin, kuma kasuwannin hada-hadar kuɗin za su farfaɗo, domin Girika tana kan kyakkyawar hanya.

To sai dai har yanzu kasuwannin na fama da rashin tabbas. Hukumar Standard and Poor's ta wargaza kyakkyawan fatan ministan sakamakon alƙalumman da ta bayar da ke nuna cewa, basussukan dake kan Girika sun kai kashi 124 cikin 100 na yawan kayakin da take samarwa wato kenan ya ninka har sau biyu adadin da aka amince da shi a tsakanin ƙasashen tarayyar takardun kuɗi na Euro. Hukumar ta ce duk da matakan tsimin kuɗi basussukan za su kai kashi 131 cikin 100, bisa dalilin cewa a dole Girika za ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen biya kuɗin ruwa. Hakan zai ƙara jefa ta cikin aƙubar bashi, inji hukumar.

Ganin cewa yanzu hukumar ta kuma rage ƙarfin biyan bashi na ƙasar Portugal, ya sa yanzu 'yan siyasar Girika sun fara samun kwanciyar hankali ganin matsalar ba ta tsaya kansu su kaɗai ba. Fatan su dai shi ne ƙungiyar EU ta gaggauta ba su taimakon kuɗin da suke buƙata.

Mawallafa: Thomas Bormann / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu