1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ta-zarce a Kongo-Brazzaville

Suleiman BabayoOctober 27, 2015

Sakamakon zaben raba gardama da gagarumin rinjaye aka amince da kwaskwarimar wa kundin tsarin mulki domin Shugaba Danis Sassou Nguesso ya tsaya takara a karo na uku

https://p.dw.com/p/1GuxS
Kongo-Brazzaville Denis Sassou N'Guesso Staatspräsident
Hoto: imago/Xinhua/H. Bing

A cewar hukumomin kasar, sakamakon ya nuna kashi 93 cikin 100 na wadanda suka fito zabe sun amince da gyara kundin tsarin mulkin da ya kawar da wa'adi da kuma shekarun da ake bukata. Hukumar zaben ta ce kashi 72 cikin 100 na wadanda suka cancanci zabe suka fito domin zaben da ya gudana a ranar Lahadi da ta gabata.

Ministan cikin gida Raymond Mboulou ya bayyana haka a tashar talabijin ta kasar. Wannan matakin ya share hanya ga Shugaba Danis Sassou Nguesso na ya sake iya tsayawa takara don yin ta-zarce a zaben badi. 'Yan adawa kuwa sun yi watsi da wannan zaben raba gardama.

Paul Melly dan jarida masanin harkokin kasashen Afirka renon Faransa a cibiyar kula da harkokin kasashen da ke birnin London, cewa ya yi:

"Babu wani abin mamaki kan sakamakon, kuma haka yake kasancewa tun lokacin da Sassou Ngesso, ya sake dawowa kan madafun iko. Farko da zaben raba gardama na amincewa da kundin tsarin mulki a shekara ta 2002."

'Yan adawa sun ce za su ci gaba da nuna tirjiya bisa wannan gyara da aka yi wa kundin tsarin mulki na kawar da yawan wa'adin da shugaba zai yi kan madafun iko na shekaru bakwai sau biyu, da fitar da yawan shekarun haifuwan dan takara, inda a baya duk dan takara da ya haura shekaru 70 ba zai yi takara ba.

Bonaventure Mbaya tsohon minista a gwamnatin kasar kana wanda yake da jam'iyyar siyasa, yana ganin zaben raba gardama tun farko ba ya kan doka:

"Kundin tsarin mulkin Kongo ya haramta duk wani kwaskwarima ga kundin tsarin mulki."

Yayin da hukumar zaben kasar ta Kongo ke cewa kashi 72 cikin 100 na masu zabe suka kada kuri'a, a daya hannun 'yan adawa na cewa kashi 10 cikin 100 kacal suka yi zaben. Hukumar zaben ta ce, fiye da mutane miliyan daya da dubu-200 suka amince da sauya tsarin mulkin, yayin da dubu-102 suka nuna rashim amincewa. A kasar mai mutane fiye da milyan hudu da rabi. Paul Melly dan jarida ya ci gaba da tsokaci

"Masu saka ido kan zabe suna da shaida cewa mutane kalilan suka fito musamman a birnin Brazzavile fadar gwamnatin kasar da suka ziyarta."

Shi dai Shugaba Danis Sassou Nguesso na kasar Kongo-Brazzaville, a farko ya mulki kasar daga shekarar 1979 zuwa 1992. Sannan ya sake dowowa kan madafun iko a shekarar 1997. Abin da ke nuna cewa, Shugaba Nguesso dan shekaru 71 da haihuwa ya mulki kasar na tsawon shekaru 31 a shekaru 36 da suka gabata.

Zürich Demonstration für die Unabhängigkeit Cabindas
Hoto: Association Cabindaise em Suisse
Wahlen im Kongo 15. Juli 2012 Wahllokal Brazzaville
Hoto: GUY-GERVAIS KITINA/AFP/GettyImages