1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Somalia

Zainab A MohammadJuly 20, 2006
https://p.dw.com/p/BvTR
Mayakan sakai a Somalia
Mayakan sakai a SomaliaHoto: AP

Kasar Habasha ta bayyana cewa tana laakari da ayyukan sabuwar kungiyar kotunan Islama dake rike da sassa daban daban na kasar da birnin Mogadisho,domin afkawa duk wanda yayi yunkurin kaiwa gwamnatin rikon kwarya a karshin jagorancin Abbdullahi Yusuf.

Ministan harkokin yada labaru na Habasa Berhan Hailu ya fadawa manema labaru a birnin Adis ababa cewa,bazasu amince da wani yunkuri na kaiwa Baidoa hari ba,a bangaren kungiyoyin Musulmi da yanzu kusan dukkan kasar ta Somalia ke karkashinsu.

Gwamnatin Habashan dai na marawa gwamnatin rikon kwarya na shugaba Yusuif baya ,wadda a yanzu keda matsugunninta a garin Baidoa,wadda kuma tayi Allah wadan ayyukan kungiyoyin sakai na musulmin ,wadanda a yanzu ke rike da akalar gudanar da Mogadisho tun daga watan daya gabata,kungiyar data kira yan tarzoma.

Yunkurin da mayakan kungiyoyin kotunan Islaman sukayi jiya ta gefen Baidoa,ya haifar da tsoro ,adangane da barkewan rikici tsakanin bangarorin biyu.

Habashan dai na lura da ayyukan yan kungiyar ,wadda a yanzu mayakanta suka koma mogadisho,sakamakon gargadin da habashan tayi musu na kada su kai hari a garin Baidoa,dake zama matsugunnin gwamnatin rikon kwarya na Somaliyan a yanzu,inji ministan yada labarai Hailu.

Yan jaridar kanfanin dillancin labaru na reuters sun tabbatar da komawan mayakan zuwa birnin na Mogadisho.

Gwamnatin na Habasha dai na taka muhimmiyar rawa a rikicin kasar ta Somalia,inda take amfani da kwararru,kana majiya na nuni dacewa tana dubban sojojinta dake cikin shirin kota kwana acikin somalian,wadanda kuma zasu iya afkawa mayakan islaman idan bukata ta taso.

Ayayinda kwararru sun sanar dacewa tana wasu dubu 20,dake jibge kan iyakar Habashan da Somalia.

A baya dai Habasha takai somame Somalia ,domin yakan sojojin sakai na Islama.

Akwai dai matakan diplomasiyya daga sassa danan daban na duniya domin warware rikicin na somaliya,kasar data fada rigingimu na yaki tun daga shekarata 1991,saboda rashin zaunanniyar gwamnati,tun bayan hanbare shugaban mulkin kama karya watau Mohammed Siad Barre.

To sai dai a ganin manazarta da kwararru dama yan kasar ta Somalia,wannan takun saka dake tsakanin kungiyoyin islaman da gwamnastin rikon kwarya dake iko kadai a Baidoa,zai ya sake jefa kasar cikin wani wadi na tsaka mai wuya na sabon yaki.adangane da hakane ministan yada labarum na Habasha,yace sunyi maraba da yunkurin kungiyar gamayyar Afrika AU dana Igad,wajen neman hanya madaidaiciya na warware rikicin na Somalia.

Kungiyoyin biyu dai sun gabatar da shirin aikewa da ayarin sojojin kiyaye zaman lafiya kasar,shirin da kungiyoyin musulmin suka nuna adawa dashi.

Habashan dai tayi imanin cewa kungiyar AU da Igad ne zasu iya warware wannan rikici da Somalia ta tsinci kanta ciki.