1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Somalia

November 2, 2006
https://p.dw.com/p/BudY

Gwamnatin riƙwan ƙwarya, a Somalia, ta yi wastsi da sabuwar shawara komawa tebrin tantanawa, da dakarun kotunan islama.

Kakakin gwamnatin, Ahmed Omar Gagale, ya rataya lefin cijewar tantanawar, a kan shugabanin kotunan Islama.

Kamar yadda ƙila, ku ka riga kuka sani, jiya ne, a ka watse baram-baram, tsakanin tawagogin 2, a taron sulhun da su ka shirya, birnin Khartum na ƙasar Sudan, bisa jagoranci ƙungiyar haɗin kan ƙasashen larabawa.

Jim kaɗan bayan wargajewar wannan taro, ministan harakokin wajen Somalia, Isma´ila Hourre Bouba, ya ce gwamnatin riƙwan ƙwarya, ta daina ɗaukar dakarun Kotunan Islama, a matsayin abokan tantanawa.

Hanya mafi dacewa da ta rage yanzu,itace kawai ɓarin wuta tsakanin ɓangarorin 2,kuma jiki magayi.

A halin da ake ciki, ɓangarorin 2, su nja daga, cikin shirin ta kwana.