Rikicin Somalia | Labarai | DW | 31.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Somalia

Prime ministan Somalia ya bayyana cewa mutanen da ake zargi da harin da aka kaiwa ofishin jakadancin Amurka hari a gabashin Afrika ,a shekarata 1998,suna boye a garin a halin yanzu a karkashin gamayyar kotunan musulmin somaliya.Prime minista Ali Mohd Gedi ya fadawa manema labaru cewa yan kungiyar Alqaeda guda uku da ake nema ruwa a jalolo a dangane da hare haren na kasashen Kenya da Tanzania,a wancan lokascin suna boye a garin Kismayo,kuma a shirye suke wajen nemosu domin kashe su.Mr Gedi yace a yau ya zasnta da jakadan Amurka na Kenya Michael Ranneberger,adangane inganta matakan tsaro kann iyakokin somaliya da Kenya,domin kada wadanda ake zargin su tsere takan iyaka.