Rikicin Somalia | Labarai | DW | 12.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Somalia

A kalla mutane 18 suka rasa rayukansu kana wasu masu yawa suka jikkata,sakamakon barkewan rikici bangarori masu adawa da juna a yankin kudu maso yammacin kasar Somalia.A daren jiya nedai wasu kabilu guda biyu dake yankin kudancin kasar sukayi arangama da juna.Daya daga cikin dottaban yankin Mohammed Bare ya fadawa kamfanin dillancin labari na AFP cewa ,mutane 18 ne aka kashe daga bangarorin biyu,ayayinda wasu 10 suka jikkata,wadanda a yanzu ke samun jinya a asibitin Dinsoor.Kasar ta Somalia dai nacigaba da fuskantar fadace fadacen kabilanci,tun bayan rushewar gwamnati shekarata 1991.