Rikicin Somalia | Labarai | DW | 19.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Somalia

Wani babban jamiin mdd yayi gargadi dangane da hali mawuyaci na balain rayuwa da alummomin somalia zasu fada ciki ,sakamakon karuwan tashe tashen hankula a wannan kasa,da gazawan hukumomin agaji wajen kai daukin abubuwan masurufi a yankuna dake fama da ringimun.Cordinatan tallafi na mdd a somali Eric Laroche,ya bayyana cewa akwai kimanin yan kasar dubu 100 wadanda ke neman gudun hijira sakamakon kazamin fada dake addabarsu,wadanda kuma ke bukatar agajin gaggawa da suka hadar da abinci da ruwan sha mai kyau, a birnin Mogadishu.Rahotanni daga kasar na nuni dacewa mafi yawansu sun kamu da cutar amai da gudawa .Mr Laroche ya bayyana cewa ,dakarun gwamnatin Somalianwadanda ke yakan mayakan sakai na islama ,suna hana kaiwa dubban yan gudun hijiran tallafin abinci.A yau din dai an kashe mutane 12 a wannan kazamin fada.