Rikicin Somalia | Labarai | DW | 14.06.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Rikicin Somalia

A birnin Mogadiscio na ƙasar Somalia, wani saban rikici ya ɓarke tsakanin dakarun gwamnati masu goyan bayan ƙasar Ethiopia, da kuma yan takifen kotunan Islama.

Daga daren jiya zuwa sahiyar yau, rahottani sun tabbatar da mutuwar mutane 2, a cikin arangamar tsakanin ɓangarorin 2.

Muntanen da su ka muntun sun hada da komishinan yan sanda, na yankin Shibis.

ƙungiyar Matasan Mujahideen, ta ɗauki alhakin wannan kissa, ta kuma yi barazanar ci gaba da kai hare-haren, har sai dakarun Ethiopia da na ƙungiyar taraya Afrika, sun ficce daga Somalia.