1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Simbabwe Krise

Stäcker, Claus / Johannesburg (SWR) neuApril 18, 2008

Tsvangirai ya yi kira da a sauke Thabo Mbeki a matsayin mai shiga tsakani a rikicin siyasar Zimbabwe

https://p.dw.com/p/DkDB
Shugaban jam´iyar MDC, Morgan TsvangiraiHoto: AP

A rikicin da ake yi tsakanin gwamnati da ´yan adawa a Zimbabwe, shugaban ´yan adawa Morgan Tsvangirai ya yi kira da a sauke shugaban Afirka Ta Kudu Thabo Mbeki a matsayin mai shiga tsakani. Ya roƙi shugaban ƙungiyar raya ƙasashen yankin kudancin Afirka kuma shugaban Zambia Levy Mwanawasa da ya karɓi ragamar wannan aiki.

A karon farko jagoran ´yan adawa Zimbabwe Morgan Changirai ya goyi da bayan kai gwamnatin Mugabe kotu. A lokacin da yake magana a birnin Johannesburg jiya alhamis, jajiberen ranar cika shekaru 28 da samun ´yancin kan Zimbabwe Changirai cewa ya yi.

"Muna duba yiwuwar kafa wata kotun majalisar ɗinkin duniya kamar irin wadda aka kafa a Saliyo da Janhuriyar demoƙuraɗiyyar Kongo. Domin dole ne a kawo ƙarshen tashe tashen hankula kuma za a iya yin haka idan waɗanda ke da hannu a ciki su kan cewa watan wata rana za su gurfana gaban ƙuliya."

Wato kenan a gurfanad da Robert Mugabe mutumin da ya jagoranci Zimbabwe ta samun ´yanci a gaban kotu? Ko kaɗan shugaban mai shekaru 84 a duniya ba ya tunanin haka, kuma har yanzu ya ƙi rungumar ƙaddara cewa ya sha kaye a zaɓe. Baya ga mawuyacin halin da ya jefa al´umar ƙasarsa ciki yanzu da ƙarfin tuwo yana son ya hana su samun abin suka zaɓa. Alƙalumman da jam´iyar MDC ta bayar sun yi nuni da cewa an kashe mutane huɗu a cikin kwanaki uku da suka gabata yayin da 200 suka samu raunuka sannan kuma aka yi awon gaba da mutane 50 a cikin matakan ba sani ba sabo da dakarun tsaro kai ɗauka kan ´yan adawa. Changirai wanda ya yi watsi da zargin da gwamnati ta yi masa na cin amana ƙasa tare da haɗa kai da Birtaniya don kifar da gwamnati, ya bayyana bukin ´yancin da za´a yi yau da cewa.

"Ko shakka babu bukin ´yancin kan na bana shi ne mafi muni tun bayan samun ´yanci daga ´yan mulkin mallaka."

Yanzu haka dai jagoran ´yan adawa na ƙoƙarin shawo kan maƙwabtan Zimbabwe da su yi sulhu tsakani da Allah. Ya yi kira ga shugaban Zambia Levy Mwanawasa wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar raya ƙasashen yankin kudancin Afirka da ya fara wani sabon shirin yin sulhu na gaskiya ba kamar shugaban Afirka Ta Kudu Tabo Mbeki ba. Changirai na mai ra´ayin cewa ganin yadda Afirka ta Kudu ta kewa Mugabe fadanci, ya kamata Thabo Mbeki ya sauka a matsayin mai shiga tsakani. Shi ma shugaban Amirka George W Bush ya yi soka lamirin wasu shugabannin Afirka da rashin fitowa fili su ƙalubalanci shugaba Mugabe. A wajen bukin cikar ƙasar shekaru 28 da samun ´yanci da za a yau Mugabe zai yi wani jawabi mai muhimmanci na farko tun bayan zaɓen na ƙarshen watan maris.