1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Rikicin siyasar Thailand

default

Rikicinsiyasa a Thailand


Bisa dukan alamu ,an kama hanyar warware rikicin ƙasar Thailand bayan da Firaminista ya amince da yin murabus da kuma matakin da masu zanga -zanga suka ɗauka na fita daga filayen saukar jiragen sama a birnin Bangkok.


Yau mako guda kenan da magoya bayan jam´iyar adawa ta PAD, suke zaman dirshin a filayen saukar jiragen sama guda biyu na birnin Bangkok, inda suka ɗauri aniyar zaman  sai inda mai ya ƙare, muddun Firaminista Somchai Wongsawat bai yi murabus ba daga muƙaminsa.

A cikin wannan yanyi ne, kotun ƙolin ƙasar yau da safe ta yanke hukunci a game da ƙarar da ´yan adawa suka shigar.

Sakamakon kotun, ya rushe jam´iyar PPP mai rike da ragamar mulki bayan binciken da kotun ta gudanar ya gano cewar ta tafka maguɗi a zaɓen watan Desember na shekara ta 2007.

A ɗaya wajen, wannan sakamakon ya haramtawa wasu gagan ´yan siyasa na jam´iyar wanda suka haɗa da Firaminista Somchai shiga harakokin siyasa har tsawan shekaru biyar.

Masu zanga zangar nuna ƙyamar gwamnati sunyi lale marhabin da sakamakon kotu, wanda jim kaɗan bayan bayyana shi ,suka yanke shawara tattanawa da hukumomin filayen saukar jiragen sama, domin fita daga ciki.

Firaminista Somchai Wongsawat, bai nuna taurin kai ba, ga hukunci kotin ƙolin, kuma ya amince yayi murabus, kamar yadda sakamakon ya umurce shi aikatawa.

Badan jam´iyar PPP hukunci ya shafi wasu jam´iyu guda biyu masu ƙawance da ita.

Kamar yadda dokokin ƙasar Thailand suka tanada, kotu na da damar rushe jam´iyar siyasa kwata-kwata da zaran binciken ya gano cewa,r ko da ɗaya daga magoyan bayanta ne ya shirya maguɗi a zaɓe.

To saidai a wani mataki na riga kafi wanda ya fi magani, tunni rukunin´yan Majalisar dokoki 216 na jam´yar PPP ya girka wata sabuwar jam´iyar siyasa mai suna Pheu Thai, wacce kuma zata naɗa saban Firaminista ta la´akari da rinjaye dake gare ta a Majalisar Dokoki.

Bayan amincewar masu zanga zangar na fita daga filayen saukar jiragen sama hukumomin  dake kula da wuraren sun bayyana yin asara mai yawa.

Rikicin ƙasa,sar ya rutsa da duban yan yawan buda ido wanda a yau suka fara fita ta hayanr wasu ƙanana filayen saukar jirage.